Hukumomi sun tabbatar da rasuwar mutane 30 a yayin da aka ceto wasu 719 da suka maƙale a saman rufin gine-gine bayan Ambaliyar Maiduguri a Jihar Borno.
Kazalika mutanen da suka maƙale a wasu wurare da ruwa ya yanke su da sauran al’umma na tsawon kwanaki na neman a kawo musu ɗaukin gaggawa, a yayin da sojoji da sauran hukumomi ke ci gaba da aikin ceto.
Har yanzu dai iyalai na ci gaba kokarin gano ƙananan yara da ’ya’yan uwansu da suka bace tun bayan tasowar ambaliyar da ta gairgiza al’ummar Najeriya da sauran wurare.
Shekara 30 rabon da Maiduguri ta shaida irin wannan ambaliya, wadda a wannan karon ta taso sakamakon ballewar Madatsar Ruwa ta Alo, kilomita 10 daga garin Maiduguri.
- NAJERIYA A YAU: Shin Dole Sai An Ɗauki Tsauraran Matakai Kafin A Saita Najeriya?
- Nan ba da jimawa ba za mu kama Bello Turji — Janar Musa
Gwamnatin Jihar Borno ta sanar cewa sama da mutane miliyan daya ne ambaliyar ta shafa, inda ta raba su da muhallansu da dukiyoyinsu.
Tuni dai aka bude sansanonin ’yan gudun hijira a sassan jihar domin tsugunar da jama’an da ambaliyar da ta taso da tsakar dare ta mamaye yankunansu.
Gwamnatin Tarayya ta ba da gudummawar Naira biliyan uku domin fara tallafa musu, a yayin da gwamnatin jihar ta fara samar musu da dafaffen abinci da kayan jinƙai.
Hukumomin agaji na ƙoƙarin ɗaukar matakai domin dakile ɓullar Cututtuka masu yaɗuwa, sakamakon yadda ruwan ambaliyan ya yi awon gaba kazantar masai da magudanan ruwa da maƙabartu da wuraren zubar da shara.
Hakazalika ana taka-tsantsan game da yiwuwar mutane su fuskanci sauran macizai da kadoji da sauran miyagun dabbobi da ambaliyar ta sa suka tsere da gidan zoo na Kyarimi.
Hukumar gidan zoo din dai ta ce ambaliyar ta hallaka kashi 80% na dabbobin, amma ta gargadi jama’a kan barazanar harin kadoji da macizai.
Zuwa ranar Laraba dai ruwan ya fara janyewa, inda wasu mutane suka samu zuwa gidajensu domin ganin halin da suke ciki ko kwasar abubuwan da za su iya.
Akasarin unguwanni a garin Maiduguri ambaliyar ta shanye su har zuwa akalla cinyar dan Adam, a wasu wuraren ma har gadoji ta shanye.
Babbar Kasuwar Monday da sauran kasuwanni da Fadar Shehun Borno da Jami’ar Maiduguri da Asibitin Koyarwa na jami’ar da unguwar manyan masu kuɗi sa wasu fitattun unguwanni a Maiduguri na daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA ta ce aƙalla iyalai 200,000 ne abin ya raba da gidajensu, inda kawo yanzu ba a iya lissafa girman barnar ba.
’Yan kasuwa a Babbar Kasuwar Monday da ke garin sun ce asarar da suka yi ta kai ta biliyoyin Naira na kayan abinci da sauran hajoji.
Gwamnatin Borno ta danganta fashewar Madatsar Ruwan Alo da ya haddasa ibtila’in da sauyin yanayi da kuma yawan ruwan da saman da aka samu a daminar bana.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya ba da tabbacin gyara da ƙara ƙarfi Madatsar Ruwa ta Alo da kuma rushe gine-ginen da ke kan hanyar ruwa.