Majalissar Dokokin Jihar Jigawa ta janye dakatarwar da ta yi wa Hon. Sani Isyaku mai wakiltar mazabar Gumel.
Dawowar Sani Isyaku Gumel ya biyo bayan rokon da dattawan Masarautar Gumel das wasu sassan jihar suka yi wa majalissar ne.
Kakakin Majalissar Dokokin, Hon. Idris Garba Kareka ya sanar da hakan a zaman majalisar da ranar Alhamis.
Hon. Idris ya kuma yi sauye-sauyen shugabannin kwamatocin majalissar, ya rusa dakatar da kwamatin bincikar Hon. Sani Isyaku.
Ya kuma soke rusa kwamatocin bincike da na aikin gona da kuma kwamitin ayyuka wanda Hon. Sani Isyaku ke jagoranta.
Rikicin dakatar da Hon. Isyaku
Majalisar ta dakatar da Hon. Sani Isyaku ne a watan Maris bisa zarginsa da hannu a ihun da aka yi wa Gwamna Badaru a garin Hadejia lamarin da ya sa majalisar ta harzuka har ta dakatar da shi.
Sakamakon haka ne ya garzaya Babbar Kotun Jihar yana neman ta bi masa hakkinsa, abin da ya sa kotun umartar majalisar ta biya shi dukkan hakkokinsa da ta hana shi.
Amma duk da wancan umarni na kotun majalissar jihar ba ta mayar da shi ba.
Ko a zaman kotun na ranar Laraba, Mai Sharia Ahmed Isah Gumel ya yi takaici yadda majalisar ta ki girmama umarnin kotun.
Ya ce idan masana doka zasu ki girmama doka, to ta yaya wanda bai san doka ba shi kuma zai yi wa dokar biyayya.
Shin an sasanta da juna?
Daga bisani majalisar ta sanar da afuwarta ga Sani Isyaku tare da janye dakatarwar, ta kuma umarce shi ya dawo majalisar.
Hakan ya biyo bayan korafe-korafe da kiraye-kirayen jama’a na neman a sasanta tsakanin bangarorrin.
Sani Isyaku ya ja daga
A jawabinsa ga ‘yan jarida Sani Isyaku Gumel ya ce shi dai ba zai janye ba saboda hakan ya zama izina ga ita gwamnatin.
Dan hakan zai magana da lauyoyinsa Kuma lauyansa zaiyi magana damu hardai zuwa lokacin damuke rubuta labarin bamu Sami jinta bakin lauyanba