An shiga rudani sakamakon hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke na korar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Abubakar Yakubu Suleiman, da mataimakinsa, Jamilu Umaru Dahiru.
Kotun wadda ta ayyana wannan hukunci a ranar Litinin ta kuma ba da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 15 na jihar.
- Tinubu zai tafi Dubai taron sauyin yanayi ranar Laraba
- Tinubu zai ranto bashin dala biliyan daya a Bankin Raya Kasashen Afirka
Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed yake shirye-shiryen gabatar wa majalisar kasafin kudin jihar na badi.
Tun a ranar Juma’ar da gabata ce kotun ta kori Kakaki Majalisar wanda yake wakiltar mazabar Ningi ta Tsakiya yayin da ta kuma kori mataimakinsa Jamilu Umar Dahiru a ranar Litinin.
Kotun ta bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfuna 10 da ke Ningi ta Tsakiya da kuma rumfunan zabe 4 da ke mazabar Birnin Bauchi.
Kotun ta kuma soke zaben wani dan majalisar mai wakiltar mazabar Zungur/Galambi/Miri, Honarabul Yusuf Saidu Ahmed na jam’iyyar PDP, tana mai ba da umarnin sake zabe a wadansu rumfunan zabe na yankin da ya fito.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, dukkan ‘yan majalisar da hukuncin kotun ya shafa ‘yan jam’iyyar PDP ne.
Sai dai jami’in wayar da kan masu kada kuri’a na Hukumar Zabe ta INEC, Aliyu Shaba, ya bayyana cewa har yanzu ba su samu umarnin kotun da ta kori shugabannin biyu ba, amma a matsayinsu na masu bin doka da oda hukumar sun shirya tsaf domin sake zaben cikin wa’adin da aka kayyade.
“Ba a ba mu umarnin kotu ba tukuna, muna jiran isowar hukuncin a rubuce, amma lauyanmu ya ce muna da kwanaki 90 kafin mu shirya sabon zabe.
“A shirye muke mu yi wa kotun biyayya. Za mu sanya ranar da za a sake gudanar da zaben.”
Da yake mayar da martani kan hukuncin, daya daga cikin lauyoyin jam’iyyar PDP, Barista Aminu Balarabe Isah, ya ce “koda yake ba mu san yadda alkalan kotun daukaka karar suka yanke hukuncin ba amma dai lamarin da mamaki, kasan alkalai na da irin idanun da suke duba hukunci.
“An ce shari’a sabanin hankali, domin a mazabar birnin Bauchi wato Bauchi ta Tsakiya APC sun kai koke ne a kan rumfunan zabe guda 9, sun kawo shaidu hudu a rumfunan zabe hudu suka bar biyar.
“Sannan dan takarar PDP ya doke dan takarar APC da tazara mai yawa. Shi ma a Zungur Galambi, jam’iyyar APC ta yi koke ne kan rumfunan zabe guda 12, inda suka kawo shaidu biyar, suka yi watsi da bakwai, su ma an kayar da su da tazara mai yawa, domin yanzu ba a bayyana adadin rumfunan zabe da za a sake gudanar da zabe ba.
“Babu takaimaimman hukuncin da alkalan suka bayar, amma za a san adadin rumfunan zaben da abin ya shafa ne a lokacin da kotu ta bayar da da hukuncinta a rubuce.”
Aminu ya ce babu wani abin fargaba domin ‘yan takararsu za su ci zabe idan hukumar zabe ta sake gudanar da zaben a rumfunan da aka ce a sake zaben.
Shi ma a nasa bangaren, lauyan jam’iyyar APC, Barista Usman Bappah Darazo, yayin da yake mayar da martani, ya ce hukuncin ya yi daidai bisa adalci.
Ya bayyana cewa hukuncin ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala kan batun zaben da akayi a wasu mazabu a Jihar Bauchi.
Ya ce kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke ta umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a wuraren da abin ya shafa.
Darazo ya ce jam’iyyar APC ta ji dadin hukuncin da aka yanke, domin hakan alama ce da ke nuna cewa zaben 2023 da aka yi a Jihar Bauchi ya kasance “da matsala.
Wasu masu fashin baki kan yadda al’amura ke gudana — Mallam Muhammad Jibril Sogiji da Mallam Ahmad Tijjani Kolo — sun ce korar kakakin majalisar da mataimakinsa ya haifar da babban gibi a shugabancin majalisar, wanda wadansu shugabannin ka iya rasa matsayinsu a majalisar.
“Kuma bisa doka ana sa ran Gwamna ya gabatar da kasafin kudin 2024 kafin karshen watan Disamba, wanda a yanzu ba za a iya gabatar da kasafin ba sai an samu shugabanci a majalisar walau a karkashin shugaban majalisar ko mataimakinsa.”
Wata majiya a majalisar ta ce ‘yan majalisar na iya zama kowane lokaci domin zabar sabon kakakin majalisar da mataimakinsa domin kaucewa barin gibi a shugabancin majalisar wanda hakan zai iya tsaida aikinta.