An shawo kan sace-sacen da aka yi ta yi a kasar Argentina lokacin da jami’an ’yan sanda suka shiga yajin aiki, har ta kai ga kafa ’yan banga wadanda suka rika bai wa gidajensu kari a birnin kurduba, wanda yake shi ne birnin mafi girma na biyu a kasar, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito. ‘’Yan sandan sun yi yajin aikin ne don neman karin kudin albashi.
Gwamnan birnin kurduba, Jose Manuel, ya cimma matsaya a yarjejeniyar da ya kulla da jami’an ’yan sandan, inda aka yi musu karin kudin albashin. Wannan tashin hankali na nuni da cewa cikin sauki da za a iya yin yamutsi a kasar Argentina. Domin mafi aywan biranen kasar zagaye suke da rukunin gidajen talakawa, wadanda ke fama da talauci a kauyuka. Shi yasa ake yawan samun zanga-zanga neman tallafin gwamnati don shawo kan hauhawar farashin bukatun rayuwa.
De la Sota, ’yar adawar siyasar Shugaba Cristina Fernandez, ta bayyana cewa an takura wa al’ummar kurduba, ta hanyar hana musu kayan more jin dadin rayuwa daga tallafin gwamnatin tarayya. Don a cewarta “kamat aya yi a shawo kan wannan tashin-tashinar ta hanyar aikewa da ‘’yan sandan kasa tun da farko.”
An shawo kan yajin aikin ’yan sanda da ya haifar da sace-sace a kasar Ajantina
An shawo kan sace-sacen da aka yi ta yi a kasar Argentina lokacin da jami’an ’yan sanda suka shiga yajin aiki, har ta kai ga…