An bukaci maniyyata Aikin Hajji mai zuwa a Jihar Kurosriba da su fara bayar da kudin ajiya tun daga yanzu na kudin Hajjin badi.
Tsarin, wanda ake kira da asusun gata, ana sa rai ga duk wadanda suke da niyyar zuwa, tun daga yanzu su fara bayar da kudinsu ta hannun hukumar jiha, kafin daga bisani kuma ita Hukumar Alhazai ta kasa ta sanar da kayyadajjen kudin kujera.
Alhaji Tanimu Hassan Shugaban Hukumar Alhazai na Jihar Kurosriba ne ya sanar da haka ga wakilinmu. Ya ce ba na “Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCO ta bullo da hanyar samar wa kanta sauki wajen rajistar mahajjata, wadda a badi maniyyaci zai yi rajista ta intanet, wanda hakan zai magance matsalar rikici da ake samu tsakanin hukumomin jihohi da mahajjata wajen biyan kudi da kuma tashin alhazai; wanda a wasu jihohin ake zargin wasu shugabannin hukumar da yin rub-da-ciki ko wala-wala da kudin mahajjata. A badi za a yi rajistar mahajjata ne ta tsarin kwamfuta yadda ba za a samu zargin bacewar kudin duk wani wanda ya biya ba,” in jishi.
Ya ci gaba da cewa: “Hukumar har wayau ta shawarci dukkannin shugabannin hukumar Alhazai na jihohi da su fara karbar kudin adashin gata daga maniyyaci da akalla Naira dubu 300 ko fiye ma, in ya so idan lokaci ya yi hukuma ta kasa ta sanar da kudin kujera, idan ma mutum ya biya kudin ajiya fiye da yadda hukuma ta kayyade, za a mayar masa da kudinsa da suka yi rara.”
Ya yaba wa shugaban hukumar na kasa bisa namijin kokarin da ya yi wajen inganta Aikin Hajiin da ya gabata, inda aka yi, aka gama lafiya.