Wata malamar makaranta ’yar kimaniný shekara 39 da haihuwa ta rasa ranta a sakamakon shake ta da wasu da ake zargi barayi ne suka yi har ta mutu a Jihar Kaduna.
Lamarin ya auku ne a makon da ya gabata, a gidanta da ke Unguwar Maigero, karamar Hukumar Chikum da asubahin ranar, bayan mijinta ya fita domin kai yara makaranta.
Marigayiyar mai suna Esther Taiwo Oloriade na da ’ya’ya biyu kuma tana aiki ne a Goodnews Academy, Kaduna.
Bayanai daga yankin sun nuna cewa tana cikin shirin zuwa wajen aiki ne lokacin da makisan nata suka shigo gidan, bayan sun kashe ta suka dauke motarta kirar Peagout 307.
Wata abokiyar aikinta ce ta lura ba ta ganta a makaranta ba, shi ne ta kirawo wayarta amma ba a amsa ba. Daga nan ne sai ta kira wayar mijinta, ta sanar da shi cewa ba su ga matarsa a makaranta ba ko lafiya.
Shi kuma sai ya kirata amma ba ta dauka ba saboda haka sai ya koma gidan domin ganin ko lafiya ba ta amsa wayarta.
“Na bar ta a gida da safiyar wannan rana tana shirin tafiya aiki, ni kuma na kwashe yara domin kai su makaranta, daga nan in wuce wurin aiki. Amma shi ne wasu suka zo suka kashe ta sannan suka dauke mata mota.
“Koda na shiga nadki na ganta ne a rataye sannan kuma duk akwai ciwo a fuskarta. Na garzaya da ita asibiti, inda aka tabbatar da cewa ta mutu. Wannan abin bakin ciki ne da ba zan manta da shi ba,” inji shi.
Aminiya ta samun labarin cewa yawan aikata laifuffuka ya karu a wannan unguwa ta Maigero, ba tare da an dauki matakin magance matsalar ba.
Tuni aka binne marigayiyar a makabartar unguwar, inda Reberend Simon Adewuyi na Cocin Baptis Kaduna ya gargadi mutane da su kauce wa aikata mugayan laifuka. A cewarsa, rayuwar duniya ba da tsawo kuma ko bajima ko badade duk mai rai mamaci ne.