An sayar da kunshin damben da Muhammad Ali ya yi amfani da su kimanin shekara 50 da suka gabata a kan Dala dubu 837 kwatankwacin Naira miliyan 130.
Rahoton da kafar sardarwar naij.com ta kalato ya nuna, kunshin ne Muhammad Ali ya yi amfani da su a karon farko a gasar dambe ta duniya bayan ya doke abokin karawarsa Sonny Linston a watan Fabrairun shekarar 1964.
A ranar Asabar da ta wuce ne aka sayar da kunshin damben marigayin a birnin New York da ke Amurka sai dai mutumin da ya saya ya ki amincewa a bayyana sunansa ko wurin da yake zaune saboda dalilai na kashin kansa.
Muhammad Ali, wanda ake wa lakabi da Cassius Clay, ya samu nasara a dambensa na farko da Sonny Linston ne a yankin Miami Beach da ke Florida a kasar Amurka a watan Fabrairun 1964.
Jim kadan bayan gama damben ne sai Manajansa mai suna Angelo Dundee ya ajiye kunshin damben a dakin ajiye kayayyakin tarihinsa. Bayan Muhammad Ali ya rasu a watan Fabrairun 2012 sai dansa ya yanke shawarar sayar da su a wannan lokaci da mahaifinsa ya cika shekara 50 da yin gasar dambensa na farko don ya samu sukunin biyan kudin asibiti ga iyalansu yayin da za a yi amfani da wani kaso daga kudin don tallafawa Cibiyar Taimakon Al’umma ta Muhammad Ali Foundation.
Mutane da yawa da kuma kamfanoni masu zaman kansu ne suka yi gogayya wajen taya kunshin damben na Muhammad Ali al’amarin da ke nuna har yanzu marigayin yana da masoya a fadin duniya.
An sayar da kunshin damben Muhammad Ali Naira miliyan 130
An sayar da kunshin damben da Muhammad Ali ya yi amfani da su kimanin shekara 50 da suka gabata a kan Dala dubu 837 kwatankwacin…