✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sauya ranar zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Jam’iyyu za su fara yaƙin neman zaɓe daga 1 ga watan Satumba sannan a kammala a ranar 25 ga Oktoba.

Hukumar Zaɓe ta Kano (KANSIEC) ta yi wani ƙwarya-ƙwaryar gyara game da ranar da za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.

Shugaban Hukumar, Faresa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Kano.

Farfesa Malumfashi ya ce sakamakon wannan canji da aka samu a yanzu za a gudanar da zaɓen ne a ranar 26 ga Oktoba, a maimakon 30 ga Nuwamba da aka sanya da farko.

A cewarsa, an yanke shawarar janyo kwanakin zaɓen ne domin yi wa Kotun Ƙoli biyayya wadda bayan nan ta bai wa ƙananan hukumomin ’yancin gashin kansu.

Ya ƙara da cewa, jam’iyyu za su fara yaƙin neman zaɓe daga 1 ga watan Satumba sannan a kammala a ranar 25 ga Oktoba.