A ranar Asabar za a yi jana’izar Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftnar Janar Ibrahim Attahiru da ’yan tawagarsa da suka rasu a hatsarin jirgin sama.
Rundunar Sojin Kasar ta ce za a gudanar da jana’izar ne a Babban Masallaci da kuma Babban Cocin Kasa da ke Abuja da misalin karfe 12.30 na rana madadin karfe 10 na safiya da aka sanar a baya.
- An yi yunkurin kashe Limamin Masallacin Harami yana cikin huduba
- Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ya rasu
Sanarwar ta ce bayan gudanar da addu’o’i, da misalin karfe daya na rana kuma za a kai mamatan makwancinsu a Makabartar Sojoji da ke Abuja.
Kazalika, za a yi Salatul Gha’ib, ga daya daga cikin mamatan, Manjo Janar Abdurrahman Kuliya bayan sallar Azahar a Masallacin Al Furqan da ke Kano, kamar yadda Limamin Masallacin kuma dan uwansa, Dokta Bashir Aliyu Umar, ya sanar.
Jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ya dauko Janar Attahiru da manyan hafsoshin soji shida da ’yan tawagarsu daga Abuja ya yi hatsari ne a yayin saukarsa a Filin Jirgi na Kaduna, Jihar da suka kai ziyarar aiki.
Sakon ta’aziyyar da Rundunar Tsaro ta Najeriya ta fitar ya ce akalla mutum 11 suka kwanta dama a hatsarin jirgin saman.
Shugaban Rundunar Tsaro ta Najeriya, Janar Lucky Irabor ya ba da umarnin a gaggauta gudanar da bincike kan abin ya haddasa hatsarin jirgin.
Jiragen soji uku ne suka fadi a 2021
Hatsarin jirgin shi ne na uku wanda jiragen sojin Najeriya suka yi a shekarar 2021.
Kafin shi, wani jirgin yaki dauke da mutum biyu ya yi batar dabo a lokacin da yake mara wa dakarun kasa baya a wani samame da suka kai wa mayakan kungiyar Boko Haram a Jihar Borno.
Lamarin da ake ci gaba da gunadar da binciki a kai ya haifar da ce-ce-kuce bayan da Boko Haram ta yi ikirarin cewa ita ce ta harbo shi.
Amma masana sun bayyana cewa bidiyon bogi ne kungiyar ta fitar cewa jirgin sojin ne da ta harbo, amma suka bukaci a yi bincike.
Kafin shi, wani jirgin soji ya yi hatsari da mutum biyar da ke cikinsa a Abuja.
Har yanzu kuma ana gudanar da bincike a kan dukkannin lamurran.