✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sauke Firaiministan Tunisia Hichem Mechichi daga mulki

Zanga-zangar adawa ta barke a kasar saboda annobar Coronavirus.

Shugaban Tunisia, Kais Saied, ya sauke Firiministan kasar, Hichem Mechichi daga kujerarsa tare da dakatar Majalisar da Dokokin kasar daga aiki.

Wannan na zuwa ne sakamakon zanga-zangar adawa da ta mamaye kasar kan yadda gwamnati ke nuna halin ko-in-kula da annobar Coronavirus.

A jawabinsa yayin wani taron gaggawa na Kwamandojin Soji, Shugaba Saied ya ce matakin na da nufin ceto kasar daga rikicin da take neman fadawa.

Kazalila, ya yi gargadi da jan kunne ga duk masu aniyar shirya wata makarkashiya da hadin bakin soji.

Sai dai Shugaban Majalisar Dokokin kasar da aka dakatar, Raches Ghannouchi, ya zargi shugaban da wuce gona da iri.

Ghannouchi ya zargi Shugaba Saied da juyin mulki kari a kan juyin juya hali da kuma tsarin mulkin kasar.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa jama’ar kasar sun barke da murna bayan samun labarin sauke Firaiministan a cikin dare.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, kawo yanzu ba a san inda Firaiministan yake ba tun bayan sanarwar sauke shi da kujerarsa.