Shugaban Tunisia Kais Sa’id ya rusa majalisar dokokin kasar wadda ya dakatar da ayyukanta tun a watan Yulin bara.
Gidan Rediyon Faransa na RFI ya ruwato cewa wannan sabon mataki da ke zuwa bayan kusan watanni takwas da dakatar da ayyukan majalisa ya kara jefa kasar a cikin wadi na rikicin siyasa.
- Sun tono gawar mahaifinsu shekara 8 da binne ta don yin tsafi
- Mahara sun kashe mutum 11 a kudancin Kaduna
Shugaba Kais ya sanar da rusa majalisar ne a jawabin da ya gabatar a daren ranar Laraba, sa’o’i kadan bayan da aka ruwaito cewa ‘yan majalisar sun gudanar da zama ta hoton bidiyo.
Yayin ganawar da suka yi, ‘yan majalisar sun sanar da cewa sun dawo bakin aiki tare da soke ilahirin dokoki na musamman da shugaban ya kafa a watanni takwas da suka gabata.