Majalisar Tsaron Jihar Borno ta sassauta dokar hana fita gaba daya da aka sanya a fadin jihar.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta sanar cewa ana a sassauta dokar ce daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3 ne bayan zaman majalisar tsaron a safiyar Juma’a.
Sanarwar da kakakin rundunar, ASP Kenneth Daso, ta bayyana cewa, “bayan zaman Majalisar tsaro kan dokar hana fita da ta sanya bayan samun rahoton cewa ’yan ta’adda na shirin amfani da zanga-zangar domin kai hari.
“An sassauta dokar da sa’o’i daga karfe 12.00 zuwa 3.00 na rana domin ba wa Musulmi damar zuwa Sallar Juma’a.
- Zanga-zanga: Jihohin da suka sanya dokar hana fita
- Zanga-zanga: An kama masu fasa shaguna 269 a Kano
“Don haka, ana bukatar mutane yi sallar Juma’a a masallatan da ke kusa da gidajensu.
“Daga karfe 3.00 na rana, dokar hana fitar za ta ci gaba da aiki zuwa karfe 6.00 na safiyar Asabar.
“Don haka ana kira ga jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu, amma su guji tayar da hankalin al’umma,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Hukumomin tsaro za su ci gaba da himmatuwa wajen tabbatar da tsaron dukiyoyi da rayukan al’ummar jihar.”