✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sare kan Alkalin wasan da ya kashe wani dan kwallo a Brazil

Kimanin makwanni biyu da suka wuce ne wani abu mai kama da al’amara ya faru a Brazil a lokacin da cacar baki ta barke  a…

Kimanin makwanni biyu da suka wuce ne wani abu mai kama da al’amara ya faru a Brazil a lokacin da cacar baki ta barke  a tsakanin alkalin wasa da kuma wani daga cikin ’yan kwallo inda ta janyo aka yi asarar rayuka.
Yadda abin ya faru kuwa shi ne, a lokacin da ake gudanar da wasan kwallon kafa na ’yan dagaji a tsakanin wadansu kungiyoyin kwallon kafa biyu sai husuma ta barke a tsakanin dan kwallo da kuma alkalin wasa a kan yadda yake yin alkalancin da bai gamsu ba.
Cacar-bakin ta yi tsananin da har alkalin wasan da kuma dan kwallon suka fara kai wa juna naushi daga bisani alkalin wasan da ya ga babu sarki sai Allah ya zaro sharbebiyar wukar da ke kugunsa inda ya rika dabawa matashin dan kwallon kuma kafin ka ce kwabo ya zubar da shi kasa warwas.  Nan da nan aka garzaya da shi asibiti amma kafin a kai rai ya yi halinsa.
Da labari ya isa filin wasan a kan mutuwar matashin ne sai wasu da ake kyautata zaton ’yan uwansa ne suka yi wa alkalin wasan dirar mikiya inda suka ja shi gefe suka yi masa duka daga bisani daya daga cikinsu ya zaro wuka ya gutsure kan kuma suka jefar da shi a tsakiyar filin wasa kafin su ranta cikin na kare.
Hakan ta tayar da hankalin daukacin magoya baya da sauran ’yan kwallon da ke cikin filin, inda koya ya kama gabansa don gudun abin da zai iya biyo baya.
Kafar sadarwar ESPN.com ta kalato alkalin wasan yana da shekara 20 kuma sunansa Octabio da Silba Catanhede Jordan da ake zarginsa da laifin kashe matashin dan kwallo mai kmanin shekara 30 mai suna Josenir dos Santos Abren. Ta ce wasan na gasar rukuni-rukuni na ’yan dagaji ne don haka gasa ce ta matasa ba ta manya ba.
Tuni jami’an tsaro suka kama mai kulob din matashin dan kwallon da aka kashe mai suna Luis Moraes Souza kuma ana neman wasu mutum biyu ruwa a jallo da ake zargin suna da hannu wajen kashe alkalin wasan da kuma guntule masa kai wadanda ake wa lakani da “Chikuinho” da “Pirolo”.
Babban jami’in ’yan sanda da ke yankin Cif balter Costa ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce  tuni rundunar ’yan sanda ta dukufa wajen zakulo wadanda suka kashe alkalin wasan don gabatar da su gaban kotu.
Al’amarin ya faru ne a filin wasa na Pius dII da ke garin Maranhao da ke Arewa maso Gabashin Brazil a ranar 30 ga watan Yunin da ya wuce.
Ya zuwa yanzu babu rahoton da ya nuna an sake kama wasu baya ga shugaban kulob din matashin dan kwallon da aka kashe.