Da yammacin Talata ne Gwamnatin Jihar Gombe karkashin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ta sake sanya dokar hana fita ta sa’oi 24 a wasu kauyuka takwas na Karamar Hukumar Balanga da ke jihar.
Sanya dokar ta biyo bayan barkewar rikicin kabilanci da ya sake aukuwa a tsakanin kabilun Lunguda da Waja da suke zaune a Karamar Hukumar Balanga ta jihar.
Dokar ta shafi kauyuka takwas ne da suka hada da Nyuwar, Jessu, Reme, Yolde Gelentuku, Sikam da kewayensu kuma dokar ta fara aiki nan take.
Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bada sanarwar sanya dokar a wata takarda mai dauke da sanya hannun Babban Darakta Kula da Harkokin Watsa Labarai na Gwamnan Jihar, Yahaya Isma’ila Uba Misilli.
Ya ce barkewar sabon rikin ne a tsakanin kauyukan ya sa aka sake sanya dokar a ranar Talata.
A cewar Farfesa Njodi, sanya dokar ya zama wajibi don ganin an shawo kan lamarin an samu zaman lafiya a yankunan da rikicin ya faru.
Kazalika, ya ce an jibge jami’an tsaro a yankunan don kwantar da tarzoma inda dokar take ci gaba da aiki har sai yadda hali ya yi
Ana iya tuna cewa, a watanin baya ne rikicin ya fara faruwa, wanda ta kai ga an yi asarar rayuka fiye da 15, lamarin da ya sanya gwamnatin ta sanya makamanciyar wannan dokar ta hana fita ta sa’oi 24.