✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sanar da ranar zaben kananan hukumomi a Kaduna

KADSIECOM ta ce za ta ba jam'iyyu akalla kwanaki 90 domin su shirya yadda ya kamata.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KADSIECOM) ta sanar da ranar 15 ga watan Mayu mai zuwa a matsayin ranar zaben Kananan Hukumomi a jihar.

Shugaban hukumar, Ibrahim Sambo ne ya sanar da hakan a lokacin da yake gabatar da jadawalin zaben ga jam’iyyun siyasa a jihar.

Ya ce kamar yadda aka tsara a jadawalin, hukumar ta fara shirye-shiryen zaben tun daga ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairun 2021, yana mai cewa a cikin makon nan za su raba wa jam’iyyun ka’idojin shiga zaben.

Ya ce hukumar za ta ba jam’iyyu akalla kwanaki 90 domin su shirya yadda ya kamata, kuma iya jam’iyyun da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta amince da su ne kawai za su fafata a zaben.

Ibrahim ya ce an tsara ba jam’iyyu damar gudanar da zabukan fid da gwani tsakanin ranakun 26 ga watan Fabrairu zuwa 28 ga watan Maris karkashin kulawar hukumar.

Kazalika, jam’iyyu za su karbi takardun tsayawa takara daga shalkwatar hukumar zaben ta KADSIECOM ranar takwas ga watan Maris.

“Za a rufe yakin neman zabe ranar 14 ga watan Mayu, 15 a yi zaben, 22 ga wata kuma a bayar da takardar lashe zabe ga wadanda suka yi nasara, sai kuma a gudanar da zagaye na biyu tsakanin 29 ga watan Mayu da biyar ga watan Yuni a wuraren da ba a sami wanda ya yi nasara ba a zagayen farko na zaben,” inji Ibrahim Sambo.