Gwamnatin Jihar Kaduna, ta bakin Kwamishinan Ilimi Usman Muhammad Makarfi, ta sanar cewa za a bude makarantu a fadin jihar daga ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba.
Kwamishinan wanda ya bayyana hakan yayin gana wa da manema labarai a kwaryar birnin Kaduna, ya ce an bai wa makarantun gwamnati da na masu zaman kansu bude wa domin ci gaba da zangon karatu na daliban Firamare da Sakandire.
Ya yi gargadin cewa dukkanin Hukumomin Makarantun su tabbatar da malamai da dalibai sun kiyaye matakan kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus kamar yadda mahukuntan lafiya suka shar’anta.
Ya bayyana cewa, za a rika gudanar da karatuttuka Safe da Yamma domin samun damar kiyaye dokar bada tazara da nesa-nesa da juna.
Sanarwar ta ce, “an sa ranar 18 ga watan Oktoba a matsayin ranar komawar daliban makarantun kwana ‘yan aji biyar na makarantun sakandire yayin da ake sa ran komar ‘yan makarantun jeka-ka-dawo daga ranar 19 ga watan Oktoba.”
“Dalibai ‘yan aji biyar da na aji biyu na makarantun Sakandire da kuma ‘yan aji shida na makarantun Firamare za su koma ne domin su zana jarrabawar kammala zangon karatuttukansu.”
Kwamishinan ya kara da cewa, daga cikin tanadin da makarantun suka yi a yanzu shi ne samar da takunkumin rufe fuska, na’urar daukan dumin jiki, da kuma wuraren wanke hannu da sabulu karkashin ruwa mai gudana.
Haka kuma ya ce za a rika gudanar da darussa kashi-kashi a lokutan mabanbanta domin rage cunkoson dalibai a cikin azuzuwa.