Yanzu haka annobar sace-sacen abubuwa da dabarun damfara ta ƙaru a tsakanin ƙananan yara da matasan Hausawa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
A wani bincike da Aminiya ta gudanar ta gano cewa ana samun yawan ɓalla ƙofofin gidaje da shaguna da ake sace kuɗaɗe da wayoyi da kadarorin ciki musamman a unguwar Sabo mazaunin Hausawa a birnin Ibadan.
- Matashi ya kashe mahaifinsa da wuƙa a Legas
- Rashin ’yan sanda ba zai hana mu zaɓen ƙananan hukumomi ba — Fubara
Binciken ya nuna cewa, a lokuta daban-daban idan asirin ɓarayin ya tonu sai a gane cewa ’ya’yan Hausawan ne suke aikata hakan ba baƙi daga waje ba.
Aminiya ta kawo misalin wata budurwa da aka sakaya sunanta wacce da rana tsaka ta sace kuɗi Naira dubu 250 a wani shagon hada hadar kuɗi (POS) inda a nan take asirinta ya tonu aka ƙwace kuɗin daga hannunta.
Kuma an samu wani mai sana’ar fawa da aka sace masa naman tsire da balangu da wuƙaƙen yankawa a cikin babban kwanon da yake ɗorawa a kansa domin talla a cikin gari.
An kuma gano wasu ƙananan yara ’yan jagora da ke musanya kuɗin sadakar da aka bayar ga iyayen gidansu makafi daga Naira 50 zuwa 10 ko daga Naira 100 zuwa 20.
Asirinsu ya sha tonuwa a bainar jama’a. Sai dai wata makauniya ta ce, “ba zan iya yin maganin wannan lamarin ba sai addu’a.”
Wani ƙaramin yaro da ya yi ƙoƙarin sayar da wayar salula mai tsada a kan Naira dubu biyar ya ƙi yin bayanin inda ya samo ta. Amma an ƙwace ta aka mayar wa ainihin mai ita bayan bincike.
A yayin binciken an gano wani wuri unguwar ta Sabo da ake kira Mutuware wanda ya zama dandalin matasan Hausawa da ya yi ƙaurin suna wajen saye da sayar da kayan sata.
Wani malami mazaunin unguwar ta Sabo, Ustaz Tahir Zubairu ya ce matsalar ta samo asali ne daga wasu iyaye musamman mata da suka kasa yi wa ’ya’yansu kyakkyawar tarbiyya kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Ya ce, “a maimakon haka ma irin waɗannan iyaye mata sun mayar da hankali ne wajen koya wa ’ya’yan nasu dabarun karɓar kuɗi daga mazajensu ta hanyar cuwa-cuwa inda yaran suke tashi da irin wannan mummunar ɗabi’a tun daga ƙuruciya.
Ya ce, “Kuma irin waɗannan ƙananan yara tun yanzu suna burin samun kuɗi ta kowace hanya ba tare da iyaye sun kwaɓe su da sanya su a halastacciyar hanya ba.”
Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban Ƙungiyar Gyaran Gari, Alhaji Ɗanjuma Garba Garas, wanda ya ce zai kira domin yin bayanin matsayin ƙungiyar a kan wannan lamari. Sai dai har zuwa lokacin rubuto wannan labarin bai kira wayar wakilin namu ba.