Miss Willie Murphy, mai kimanin shekara 77 ta tsunduma cikin harkar dage karfe mai mauyi da aka fi sani da Weightlifting a Turanci ba tare da wata matsala ba.
A halin yanzu tsohuwar tana zaune a a garin Rochester da ke birnin New York na Amurka.
A ’yan shekarun baya ne dai tsohuwar ta fara wannan harka ta daga karfe mai nauyi bayan a wani filin atisaye na masu daga karfe mai nauyi inda take zuwa tana kallo a duk lokacin da ba ta da aiki, saboda sha’awa. Ana cikin haka ne sai kwatsam ta yanke shawarar ta shiga don a dama da ita.
A lokacin da ta tuntubi manajan da ke kula da cibiyar wasan dage karfen ce sai ta shaida masa aniyarta na shiga don a dama da ita, inda nan da nan Manajan ya yi maraba da ita kuma tun daga wancan lokaci ne ta cigaba da halartar cibiyar babu kakkautawa. Kafin wani lokaci sai tsohuwar ta yi suna, inda labarinta ya bazu kuma jama’a musamman matasa suka rika kwarara cibiyar don ganin yadda tsohuwar ke ba maza kashi a harkar daga karfe mai nauyi.
Abin mamaki da al’ajabi shi ne yadda tsohuwar takan daga karfen da ya fi karfin wasu daga cikin matasan da ke halartar cibiyar inda wasu ke tunanin ko tana amfani da rafanai ne maimakon karfin tuwon da Allah Ya ba ta.
Rahoton ya nuna, nauyin gyatumar bai wuce kilogiram 40 ba, amma takan daga karfen da nauyinsa ya kai kilogiram 90.
A bara tsohuwar ta lashe gasar daga karfe mai nauyi na duniya da ya gudana a Amurka da hakan ya sa ta kara samun daukaka a sassan Amurka da ma a duniya.
Ta ce tana jin dadin yadda matasa masu karfi a jika suke tururuwa suna zuwa cibiyar don ganin yadda take wasa. “Yadda matasa ke zuwa kallon yadda nake wasan daga karfe mai nauyi abin yana burge ni don hakan zai sa da yawansu su shigo harkar don za su ce a matsayinsu na matasa mai zai hana su shiga harkar tun da ga ni tsohuwa mai kusan shekara 80 ana damawa da ni”?, inji ta.
Ta ce a mafi yawan lokaci ita kadai takan ciro motarta daga tabo idan ta kafe a lokacin damina ba tare da neman taimakon wani ko wasu ba, tun da Allah Ya hore mata karfi.
“Ban da karayar zuciya duk harkar da na kuduri aniyar yi, nakan yi ta ne kai tsaye ba tare da shakkar komai ba kuma nakan samu nasara”.
Sai dai rahoton da kafar sadarwar Naij.com ta kalato a kan wannan tsohuwa bai ambaci ko tana da miji ko ’ya’ya da jikoki ba, al’amarin da ya sa ake hasashen ita kadai take rayuwa a katafaren gidanta.
Shi ma manajan nata da aka tuntube shi a kan yadda tsohuwar ke wasa a karkashin kulawarsa a cibiyar daga karfe mai nauyi ya ce: “Tun lokacin da tsohuwar ta tuntube shi tana son ta shiga harkar wasan dage karfe mai nauyi ya amince, kuma hasalima ta fara ne ba tare da ya koya mata yadda abin yake ba. Da ta fara iyawa ne yake dora ta a hanya idan ta yi kuskure, tun da dama ba harkar ta ba ce. Da tafiya ta yi nisa ne ya yanke shawarar mayar da ita daya daga cikin daliban da yake horar da su kuma ga shi ta samu daukaka har sunanta ya mamaye sassan duniya a matsayin kwararriyar mai wasan dage karfe mai nauyi. Kuma ina alfahari da ita”, inji shi.
Yanzu dai dattijuwar ta kasance ita ce ke rike da kambun tsohuwar da ta fi kowacce kwarewa a gasar daga karfe mai nauyi a duk fadin duniya. Hakan ya sa ta shiga kundin tarihi a littafin Guiness Book of Record.