✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu wagegen gibi a kasafin kudin Saudiyya

A farkon makon nan ne kasar Saudiyya ta sanar da samun gibi har na Dala biliyan 98 (kimanin Naira tiriliyan 24) a kasafin kudinta a…

A farkon makon nan ne kasar Saudiyya ta sanar da samun gibi har na Dala biliyan 98 (kimanin Naira tiriliyan 24) a kasafin kudinta a bara, sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya.
Har ila yau, Saudiyya ta yi hasashen samun wani gibin har na Dala biliyan 87 a kasafin kudin kasar na bana, wanda shi ne gibi na uku da kasafin kasar yake yi a cikin shekara uku a jere, kamar yadda BBC ya bayyana.
Ma’aikatar Kudi ta kasar ta ce za ta sake duba  tallafin da ake bai wa sha’anin lantarki da na man fetur, sannan a sayar da wasu sassan gwamnati ga masu zuba jari.
Sai dai masu sharhi kan al’amura na kallon kudin da Saudiyyar ke kashewa a yakin da take yi da Houthi  a kasar Yemen, a matsayin makasudun samun wagegen gibin.