Hukumar da ke Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum guda mai dauke da cutar Coronavirus a Abuja.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
“An tabbatar da wani sabon kamuwa da COVID-19 a Yankin Babban Birnin Tarayya”, inji sanarwar.
Hakan ya kawo yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a yankin zuwa hudu, yayin da adadin wadanda aka tabbatar a kasa gaba daya ya kai 27, inji hukumar ta NCDC.
Daga cikin 27 din dai an salami mutum biyu bayan sun yi jinya. Har yanzu dai ba a samu wanda ya mutu ba a Najeriya sakamakon kamuwa da cutar.
An samu mutum 10 ɗauke da Coronavirus a Abuja da Legas
Coronavirus: Hukumar jiragen kasa ta lashe amanta
Kafin wannan na babban birnin Najeriyar dai, a jihar Oyo ma dai an tabbatar da samun mai dauke da cutar.
A yanzu dai 19 daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya a jihar Legas suke, hudu a Yankin Babban Birnin Tarayya, biyu a jihar Ogun, yayin da jihohin Ekiti da Oyo ke da guda ko wanne.
Tuni dai hukumomi a Najeriyar suka rufe daukacin filayen jirgin sama na kasar ga jiragen da ke shigowa daga waje.
An kuma shawarci wuraren ibada da su guje wa tara mutane fiye da 50 a lokaci guda; yayin da aka rufe makarantu a jihohi da dama.