A daidai lokacin da Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ke bayar da sanarwar ta zabi mutane 15 da za su rike mata shugabancinta karkashin jagorancin Alhaji Abdullahi Abbas, a daya bangaren kuma uwar jam’iyyar ta kasa ta bayyana cewa ba ta yanke hukunci game da batun shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano ba.
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Asabar ne Jam’iyyar ta APC reshen Jihar Kano ta gudanar da zaben jam’iyyar a dakin taro na Sani Abacha bisa sa idon tawagar Nwoko Orinze, inda aka zabi Abdullahi Abbas wanda ya dauki tsawon lokaci yana jagorantar jam’iyyar a matsayin rikon kwarya da kuri’u 2,000 daga cikin daliget 2,820 da suka kada kuriarsu.
Dama dai an dauki tsawon lokaci ana rigingimu tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Gwamnan, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso. Wakilanmu sun rawaito cewa zaben an shirya shi ne don cike gurbin manyan mukaman Jam’iyyar.
Sauran wadanda aka zaba sun hada da Alhaji Shehu Maigari a matsayin Mataimakin Shugaban Jam’iyya da Ibrahim Zakari Sarina a matsayin sakatare da Ahmed Muhammad Speaker a matsayin sakataren tsare-tsare.
Har ila yau an zabi Barista Jamilu Rano a matsayin lauyan jam’iyyar da Alhaji Sabo Mohammed Dantata a matsayin Shugaban Yankin Arewa ta tsakiya da Musa Lawan Nana Sakataren Yankin Kano ta Arewa da Ma’aruf Abdullahi a matsayin Mataimakin Shugaban Matasa da Injiniya Bashir Yahaya Karaye a matsayin Jami’in Hulda da Jama’a.
A takardar da Jami’in Hulda da Jama’a na Jam’iyyar Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu ta shawarci ‘ya’yan jamiyyar da dukkan masu ruwa da tsaki da sauran al’umma da su yi wasti da duk wani labari da suka ji cewa an cire Alhaji Umar Haruna Doguwa daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar APC. “Muna sanar da jama’a cewa babu wani mataki da kwamitin koli na jamiyyar APC ya yanke game da shugabancin Jihar Kano. Muna sane da dukkan abubwan dake faruwa a jihar. Muna kokarin samun mafita akan lamarin.
Don haka abin da yake akwai shi ne abin da muka sani tun farko har zuwa lokacin da abubuwa za su kammala” Inji takardar. Idan za iya tunawa sabanin dake tsakanin tsohon Gwmana Kwankwaso da Gwaman Gnaduje shi ya jwo aka cire Shugaban jam’iyyar ta APC, Alhaji Umar Doguwa wanda aka maye gurbinsa da Abdullahi Abbas wanda yake na hannun daman Gwamna mai ci.
Aminiya ta lakanci cewa lokacin da tawagar ‘ya’yan jam’iyyar na Arewa maso Yamma karkashin Shugabancin Sanata Magoro suka ziyarci Jihar Kano sun bayyana cewa cirewar da aka yi wa Doguwa tana kan layi.
A wata takarda mai dauke da sa hannun Ma’ajin Jam’iyyar na kasa Alhaji Bala Mohammed Gwagwarwa da kuma Shugaban cirarren Jam’iyyar Alhaji Umar Doguwa suka rubuta ga Shugaban Jam’iyyar na kasa Cif John Odigie-Oyegun a ranar 27 ga watan Janairun 2017 inda suka nuna kin amincewarsu game da yanke hukunci da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na kasa bangaren Arewa Maso Yamma, Alhaji Inuwa Abdulkadir ya yi na nada Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na Kano.