An samu sababbin masu dauke da cutar Coronavirus mutum 10 a Najeriya.
Uku daga cikin mutanen a Abuja aka same su yayin da sauran ke Legas.
Hukumar Yaki da Cututtuka masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce, ta bayyana haka a shafinta na Twitter.
“Tara daga cikin mutanen sun yi tafiya zuwa wajen Najeriya a cikin mako guda da ya gabata, na goman ba kuma na da alaka da wani wanda aka tabbatar yana da cutar,” in ji NCDC.
Zuwa yanzu an samu mutum 22 ke nan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin Najeriya.
Hukumar ta NCDC ta kara da cewa, ana kula da wadanda abin ya shafa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada a Abuja, da kuma Asibitin Kula da Masu Cututtukan da ke Yaduwa a Legas.
Wasu rahotanni sun ambato wani asibiti a birnin Abuja yana cewa, daya daga cikin mutanen da suka kamu a Abuja ya dawo ne daga Birtaniya, ko da yake mai dakinsa da suka dawo tare ba ta dauke da cutar.
Rahotannin sun kuma ce mutumin ma’aikaci ne a Hukumar Tara Kuɗin Haraji ta Tarayya, FIRS.
Sai dai hukumar ta FIRS ta musanta rahotannin, tana cewa babu ma’aikacinta da ke dauke da cutar.
A wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce abin da ta tabbatar shi ne “Wani ma’aikacinmu da ya je filin jirgin sama don dauko maidakinsa wacce ta yi tafiya zuwa waje, daga shi har ita sun killace kansu, kamar yadda gwamnati da shawarci ‘yan kasa”.
A yunkurin hana cutar yaduwa dai hukumomi a Najeriya sun bayar da umarnin rufe makarantu da wuraren taruwar jama’a ciki har da wuraren ibada.
Sai dai wasu ‘yan Najeriyar na ganin hakan a matsayin fargar jaji saboda a tunanin su tun bayan da aka samu wani dan kasar Italiya da cutar ya kamata a rufe daukacin iyakokin kasar.