An samu wata yarinya ’yar shekara shida dauke da kwayoyin cutar coronavirus a jihar Jigawa.
Kwamishinan lafiya kuma shugaban kwamitin yaki da annobar COVID-19 na jihar Dokta Abba Umar Zakari, wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce an gano yarinyar tana dauke da cutar ne bayan an sakamakon gwajin da aka yi wa mutane 18 da suka yi mu’amala da mahaifinta ya fito.
Kwamishinan ya ce sakamakon sauran mutane 17 din ya nuna ba sa dauke da cutar.
Bayan mahaifin yarinyar ya dawo daga ganin gida a kudu maso gabashin Najeriya ne dai aka tabbatar yana dauke da cutar a garin Kazaure.
A cewar Dokta Zakari, tuni aka kammala shirye-shiryen kai yarinyar wurin da ake killace wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar don kula da lafiyarta.
A yanzuhaka dai alkaluma sun nuna akwai mutane kusan 39 da suka kamu da cutar a jihar Jigawa.