✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu kamfanin Facebook da laifin sayar wa Amurka bayanan jama’a

An bukaci Facebook ya biya Euro biliyan 1 da miliyan 200 a matsayin tara.

Hukumar da ke Bayar da Kariya ga Bayanan Jama’ar Turai ta samun kamfanin Facebook da laifin nadar bayanan kasashen Turai tare da sayar wa Amurka, lamarin da ya saba da dokokin bayar da kariya ga bayanan jama’a.

Hukumar Bayar da Kariya ga Bayanan Jama’a ta Ireland DPC ce ta sanar da hukuncin ranar Litinin a madadin kasashen Turai.

DCP ta bayyana cewa hukumar kare bayanan jama’a ta Tarayyar Turai EDPB, ta bukaci lallai kamfanin na Facebook ko kuma Meta ya biya Euro biliyan 1 da miliyan 200 a matsayin tara saboda samun sa da wannan laifi.

Hukumar ta DPC ta samu kamfanin na Facebook ko kuma Meta da laifin nadar bayanan jama’ar tun daga shekarar 2020 wadanda ta mika ga Amurka.

Haka kuma, mahukuntan kamfanin da ke shalkwatarsa a Dublin sun gaza bayar da cikakken bayani game da hadari da kuma take hakkin da ke tattare da aika-aikar kamar yadda Kotun Turai ta bukata a baya.

Tuni dai kamfanin na Meta ko kuma Facebook da aka fi sanin sa da shi, ya yi kakkausar suka kan wannan hukunci, wanda ya bayyana da nuna masa wariya tsakanin takwarorinsa na kamfanonin sada zumunta da dukkaninsu ke nadar bayanai.

Shugaban sashen hulda da jama’a na Meta, Nick Clegg, ya bayyana cewa za su daukaka kara game da hukuncin yana mai cewa, babu wani batu mai kama da nadar bayanai da kamfanin ya yi a baya-bayan nan.

Adadin tarar ta fi girma fiye da hukuncin dala biliyan 800 na kamfanin Amazon, a cikin shekarar 2021 kan keta kariyar bayanai.