Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabin da ba a taba gani ba cikin shekara 27 a Najeriya.
NBS ta ce hauhawar farashin na watan Disamban 2023 zuwa kashi 28.92 ya haifar da tsadar rayuwa, kuma watanni 12 da ya yi ta tashi a jere, inda a watan Nuwamba ya kai kashi 28.20.
- Hakkin Mallaka: Kotu ta dage karar da mawaki ya shigar da BBC
- ’Yan sanda sun hallaka shugaban kungiyar asiri a Ribas
Rabon da a samu irin wannan hauhawar farashi tun 1996.
NBS, ta ce hauhawar farashi a Najeriya ya tashi zuwa kashi 33.93 a watan Disamba daga kashi 32.84 a watan Nuwamba.
Hukumar ta ce kayayyakin da farashinsu ya yi tashin gwauron zabi sun hada da burodi, hatsi, mai, kifi, nama, kayan itace, kwai da sauransu.
A gefe guda kuwa, masana sun alakanta hauhawar farashin da karuwar kudin man fetur sakamakon cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi.
Kazalika, masanan sun ce karyewar darajar Naira na daga cikin abubuwan da suka janyo hauhawar farashin.
Tsadar rayuwar dai ta haifar da tsananin wahala a tsakanin talawakan Najeriya, lamarin da ya sanya suke kiran gwamnati ta yi wani abu kai.
Idan ba a manta ba, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun bukaci Shugaba Tinubu da ya sake kan wahalhalun da cire tallafin man fetur ka iya haifarwa.