✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An samu bullar Zazzabin Lassa a Jihar Nasarawa

an kwantar da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a wani asibiti, akwai kuma wadanda ake jiran sakamakon gwajin cutar da aka yi musu

Hukumomin lafiya a Jihar Nasarawa sun tabbatar da bullar kwayar cutar Zazzabin Lassa mai kisa a jihar.

Gwamnatin jihar ta ce cutar ta kwantar da mutum biyu a asibiti, baya ga wasu mutum uku da ake zargi da alamun kwayar cutar.

Babbar Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Dokta Janet Angbazo, ta ce “An tabbatar da kamuwar mutum biyu, akwai wasu uku kuma da ake zargi sun harbu da cutar kuma ana lura da su a cikin jihar nan.”

A cewarta an kwantar da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ne a wani asibiti a Abuja, sannan ta gargadi jama’ar jihar ta su yi hattara da kamuwa cutar.

Da take sanar da haka ranar Juma’a, ta bayyana cewa an dauki samfurin jinin karin wasu mutane da ake zargi da kwayar cutar zuwa dakin gwaje-gwajen Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) domin tantancewa.

Gwamnatin jihar, a cewarta, tana shirin fara yi wa mutane gwajin kwayar cutar Zazzabin Lassa a cibiyar binciken cututtuka masu yaduwa ta jihar (NASIDARC).

“Alamomin cutar sun hada da zazzabi na mako daya zuwa mako uku bayan kamuwa da kwayar cutar.

“Kashi 80 cikin 100 na alamomin cutar Lassa ba su bayyana ta yadda za a iya gane su.

“Kashi 20 cikin 100 na masu cutar na iya fama da zazzabi mai tsanani, sarkewar numfashi, amai, jijjiga, kumburin fuska, da kuma ciwon kirji da baya da mara.

“Cutar na iya yin kisa a sakamakon daina aikin wasu sassa na jikin dan Adam,” kamar yadda ta bayyana.

Don haka ta shawarci jama’ar jihar da su dauki kwararan matakan kariya ta hanyar nisantar masu cutar gami da tabbatar da tsaftar muhalli domin kawar da beraye da dangoginsu.

%d bloggers like this: