✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu baraka a tsakanin ’yan adawa a Jihar Oyo

An samu baraka a tsakanin ’ya’yan  jam’iyyun adawa a Jihar Oyo bayan da tsohon Gwamnan Jihar kuma dan takarar Gwamna a  Jam’iyyar ADP a zaben…

An samu baraka a tsakanin ’ya’yan  jam’iyyun adawa a Jihar Oyo bayan da tsohon Gwamnan Jihar kuma dan takarar Gwamna a  Jam’iyyar ADP a zaben gobe Asabar Cif Christopher Adebayo Alao Akala ya bayyana ficewarsa daga gamayyar jam’iyyun adawa ya koma Jam’iyyar APC da ke mulkin jihar. Da yake bayyana dalilin ficewarsa daga cikin ’yan hamayyar Adebayo Alao Akala ya ce, “Kalaman bangaranci da tsohon Gwamna Rashid Ladoja yake yi a wajen taron da muke yi cewa lallai ne mu goyi bayan dan asalin Ibadan a matsayin dan takarar Gwamna yana daga cikin dalilan da suka sa na fice daga cikin wannan gamayyar jam’iyyu 5 a Jihar Oyo.”

Tsohon Gwamnan ya ce, a daidai wannan lokaci ne kuma Jam’iyyar APC ta fara zawarcinsa inda ya kai ga gayyatarsa zuwa fadar Shugaban Kasa. Ya ce, hakan ne ya sa ya yanke shawarar ficewa daga hadakar jam’iyyun adawa na PDP da ADC da SDP da ZLP domin hada kai da dan takarar Gwamna na APC Adebayo Adelabu a zaben gobe.

Adebayo Alao Akala ya ce, bai fita daga jam’iyyarsa ta ADP ba, amma shi da dimbin magoya bayansa za su mara wa Adebayo Adelabu na APC baya domin tabbatar da samun nasararsa a zaben na gobe.

Ya ce, fafutikar ci gaban al’ummar jihar ce a gabansa ba miliyoyin kudi da ake cewa ya karbo daga fadar Shugaban Kasa ba.

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa, duk da yake jam’iyyun hamayyar ne suka goyi bayan PDP ta yi nasarar lashe zaben Shugaban Kasa a jihar ba tare da yin nasara a zaben ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa ba wanda  APC ta lashe mafi yawan kujerun, ’yan takarar Gwamnan Jihar da suka hada da Seyi Makinde na PDP da Femi Lanlehin na ADC da Bolaji Ayorinde na SDP da Sharafadeen Alli na ZLP sun yanke shawarar yin taron dangi domin sake kayar da APC a zaben na gobe a jihar Oyo. Sai dai ficewarAlao Akala dai ta haifar da koma bayan fafitukar da suke yi. Kuma rashin ganin dan takarar Gwamna na ADC Sanata Femi Lanlehin a wajen taron karshe da jam’iyyun suka yi a ranar Asabar ya haifar da tababar yiwuwar taron dangi musamman saboda rade-radin cewa ba za a yi wannan tafiya tare da Femi Lanlehin na ADC ba domin zai ci gaba da fafutikar tsayawa takarar Gwamna ko ya amshi goron gayyatar da APC take yi masa.

Rashin halartar Sanata Femi Lanlehin taron na ranar Asabar, bai hana jam’iyyun PDP da SDP da ZLP ci gaba da tattaunawa ba, inda a karshe suka yanke shawarar goyon bayan dan takarar Gwamna na PDP Mista Seyi Makinde a fafatawar ta gobe.

Dukan ’yan takarar Gwamna su biyu Cif Adebayo Adelabu na APC da Mista Seyi Makinde na PDP ’yan asalin birnin Ibadan ne kuma ba su yi fice a cikin harkokin siyasa ba domin wannan ne karo na farko da suka fara bayyana kansu ga al’ummar jihar. Ana ganin kasancewar Adebayo Adelabu a matsayin tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da Seyi Makinde a matsayin fitaccen attajiri zai sa zaben na gobe ya yi zafi a fannin amfani da kudi wajen neman goyon baya jama’a.

Sai dai dukkansu ba su goyi bayan yin amfani da kudi wajen sayen jama’a ba amma sun ce irin ayyukan taimakon jama’a da suka yi a baya a sassa daban-daban na jihar sun isa shaidar cewa za su yi wa jihar aiki ne tsakani da Allah domin samun ci gabanta.