An sami fashewar wani abu a cikin wani jirgin ruwa dab da tashar jiragen ruwa dake kusa da birnin Jidda na kasar Saudiyya a ranar Litinin.
Wani kamfanin hada-hadar jiragen ruwa mai suna Dryad Global shine ya tabbatar da hatsarin a shafinsa na intanet.
- An gabatar da Sallar Rokon Ruwa a Saudiyya
- CIKIN HOTUNA: Irin barnar da fashewar ammonium ta yi a Lebanon
A cewar kamfanin, fashewar ta faru ne a cikin wata tankar mai dake kan jirgin ruwan da misalin karfe 11:11 na daren ranar Lahadi.
“Rahotanni sun nuna cewa an sami fashewar ne lokacin da jirgin ke kokarin sauke tankokin a tashar jiragen ruwa ta birnin Jidda,” inji kamfanin.
Sai dai kuma kamfani da ya mallaki tankar man mai suna Hafnia a wata sanarwa ya ce wani abu ne ya fado wa tankar wanda hakan ya jawo fashewarta tare da tashin gobara.
Kamfanin ya ce dukkan ma’aikatan jirgin 22 sun kubuta ba tare da jin ko da kwarzane ba, ko da yake wani sashe na jikin jirgin ya lalace.
“Wani abu ne ya fado wa jirgin wanda ke dauke da tan 60,000 na man fetur lokacin da yake kokarin sauke kaya da misalin karfe 11:11 na dare wanda ya yanyo hatsarin,” inji kamfanin Hafnia.
Hatsarin dai na zuwa ne a daidai lokacin kwarin gwiwar da ake da shi a kan samun rigakafin cutar COVID-19 ya daga darajar farashin man fetur zuwa sama da Dala 50 a kan kowacce ganga a kasuwar duniya.