A ranar Talatar da ta wuce ne aka sallami shahararren dan kwallon duniya kuma haifaffen Brazil Pele daga wani asibiti a Brazil bayan an yi masa aikin cire duwatsu a kodarsa.
dan shekara 74 ya harbu da cutar ce a lokacin da ake masa wata tiyata ta daban al’amarin da ya sa aka cigaba da kwantar da shi don sake yi masa aikin cire duwatsu a kodar tasa.
Idan ba a manta ba, Pele dai an taba yi masa aiki a mafitsararsa a lokacin da yake ganiyar yin wasan kwallo a lokacin da yake matashi.
“Na yi matukar farin cikin ganin yadda dimbin jama’a suka damu da rashin lafiyata kuma ina goduya a garesu saboda yanzu na samu sauki har an sallame ni. Hasalima yanzu na fara tunanin halartar gasar wasanni ta Olamfik da za a yi a shekara mai zuwa”, inji Pele kamar yadda wata jarida da ake bugawa a Brazil mai suna O. Golobo ta kalato.
An kwantar da Pele a asibiti ne kimanin makwanni biyu da suka wuce.
An sallami Pele daga asibiti 1
A ranar Talatar da ta wuce ne aka sallami shahararren dan kwallon duniya kuma haifaffen Brazil Pele daga wani asibiti a Brazil bayan an yi…