Shugaban Togo, Faure Gnassingbe, ya sallami Ministar Tsaron Kasar, Marguerite Essossimna Gnakade tare da Babban Hafsan Sojin Kasar, Janar Dadja Maganawe.
Fadar Shugaban kasar ta ce ba a nada wanda zai maye gurbin Marguerite Gnakade ba, don haka Rundunar Tsaron kasar za ta rika karbar umarni ne kai-tsaye daga Shugaba Faure.
Sanarwar, wadda aka fitar ta kafar talabijin a ranar Alhamis ta ce, “An sallami Marguerite Essossimna Gnakade daga aikinta a Ma’aikatar Tsaro.”
Ta kara da cewa an daga likafar Kanar Tassounti Djato, tsohon Shugaban Ma’aikatan Rundunar Sojin Sama zuwa mukamin Janar, “an kuma nada shi a matsayin Sabon Shugaban Ma’aikatan Soji,” ya maye gurbin Janar Dadja Maganawe, wanda ke rike da mukamin daga 2020.
Sanarwar gagarumin sauyin ba ta bayyana dalilin daukar matakin ba, duk da cewa ya zo ne a daidai lokacin da kasarke fuskantar karin barzanar ayyukan masu ikirarin jihadi.
Barazanar tsaro a Togo
Daga 2021 zuwa yanzu mayakan Jihadi sun kai hare-hare sama da biyar a sassan kasar Togo, ciki har da wadansu munana a Arewacin kasar, mai iyaka da Burkina Faso, wadda ita ma take mafa da matsalar.
Kasashen yankin Sahel da suka hada da Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar suna fama da matsalar mayakan Jihadi, lamarin da ya sa makwabtansu na Benin, Ghana, Togo da Kwaddibuwa ke tsoron tsallakowar matsalar zuwa cikin kasashensu.
A watan Yuli wasu mahara suka kai farmaki a Togo, suka kashe mutane da, suka jikkata wasu; kafafen yada labaran kasar sun ce fararen hula akalla 15 ne suka rasu a hare-haren.
A watan Nuwamba kuma aka kai wani harin a yankin Arewacin Togo, amma hukumomin kasar ba su ba da bayani a kan abin da ya faru ba.