Ragowar mutum biyar daga cikin 19 da aka sace a kusa da Dutsen Zuma da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna sun koma wajen iyalansu bayan shafe kwana uku a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
An sace mutanen ne wadanda wadansu daga cikinsu ’yan kasuwa ne wadansu kuma ma’aikata, a ranar Talatar makon jiya a kusa da dutsen da ke kusa da shingen sojoji da misalin karfe 8 na dare.
Daya daga cikin wadanda aka sacen mai suna Muhammad Mustafa wanda dan kasuwa ne a Kasuwar Wuse, Abuja, ya shaida wa wakilinmu a shekaranjiya Laraba bayan an sako su cewa wadanda suka sace su din da adadinsu ya kai 10 kuma wasu daga cikinsu ke sanye da kakin soja da bindigogi, sun wuce da su zuwa wani daji da ke da tazarar kilomita 5 daga titin, inda bayan kamar sa’a guda sai suka sako mutum 14 bayan tantance su.
“Sun kara yin gaba da mu a cikin dajin, kuma a ranar Juma’a sai suka rako mu ta bangaren garin Gauraka inda suka sako mu, mu hudu bayan sun karbi kudin fansa,” inji shi.
Ya ce ’yan bindigar sun karbi Naira miliyan bibbiyu daga hannun iyalan mutum 2 daga cikinsu, a yayin da suka karbi Naira dubu 300 da dubu 200 daga iyalan ragowar mutum biyu. Ya ce mutum na biyar ya samu nasarar kubucewa kwana guda kafin sako su.
Ya ce ya samu nasarar yin hakan ne lokacin da barci ya kama daya daga cikin barayin da aka bari ya yi gadinsu, lokacin da sauran ke kan tsaunuka da ke da dan tazara daga wurin.