✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sako tsohon shugaban ma’aikatan Taraba bayan biyan Naira miliyan 20

Masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da tsohon shugaban ma’aikatan jihar Taraba Alhaji Aminu Jika, lokacin Gwamnan Taraba marigayi Danbaba Suntai, wanda aka…

Masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da tsohon shugaban ma’aikatan jihar Taraba Alhaji Aminu Jika, lokacin Gwamnan Taraba marigayi Danbaba Suntai, wanda aka yi garkuwa da shi kwana biyar da suka wuce an sako shi a daren jiya Juma’a bayan biyan kudin fansa Naira Miliyan 20.

Aminu Jika, wanda mutumin Gwamnan jihar ne mai ci Darius Ishaku, an yi garkuwan da shi ne lokacin yana gidansa da ke unguwar Magami a cikin Jalingo babban birnin jihar.

Masu garkuwan sun yi magana da iyalan Aminu Jika, ta wayar salularsa kafin su bukaci biyan kudin fansar shi na Naira Miliyan 20.