An saki Shugaban katafaren famfanin kera wayoyin Samsung, Lee Jae-yong daga kurkuku bayan da ya samu afuwar Shugaban Kasar Koriya ta Kudu.
Ma’aikatar shari’ar kasar ta ce an yi wa attajiri Lee Jae-yong afuwa ne domin ya zo ya ba da gunmawarsa wajen tayar da komadar tattalin arzikin kasar.
- Gwamnati ta yi gargadi kan shan ruwan rafin Osun
- An ba dan sanda kujerar Hajji da N250,000 saboda mayar da dalolin tsintuwa
A shekarar da ta gabata ne aka garkame attajirin a kurkuku bayan samun shi da aikata laifuka masu nasaba da almundahana da cin hanci.
Ma’aikatar ta ce Lee ya samu afuwar ne a ranar Juma’a bayan da ya shafe wata 18 a gidan yari, wato kusan rabin wa’adin da aka yanke masa na zaman gidan kaso.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ta saki wasu tsoffin gwamnonin kasar da aka daure bisa laifin wawushe dukiyar gwamnati, wanda tuni har sun soma kwadayin tsayawa takara a yankunansu.
Ma’aikatar ta ce matsalar tattalin arzikin da duniya ke fuskanta ta yi tasiri a kan tattalin arzikin kasar wanda ya zama wajibi ta lalubo hanyar da za ta daidaita tattalin arzikinta.
Bayanai sun ce arzikin da kamfanin Samsung ke da shi ya kai daya bisa biyar na arzikin Koriya ta Kudu baki daya.