Hukumar Gyara Hali ta Najeiya ta tabbatar da sakin tsohon Gwamnan Jihar Abia Sanata Orji Uzor Kalu daga gidan yari na Kuje.
A jiya Talata ne Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da umarnin sakin tsohon gwamnan daga kurkuku bayan lauyansa, Lateef Fagbemi ya bukaci hakan.
Hukuncin kotun na sakin Kalu ya biyo bayan soke daurin shekara 12 da aka yi masa bisa aikata zambar Naira biliyan 7.1 a zamanin mulkinsa a jihar.
A watan Disamban bara ne kotu ta yanke masa hukuncin bayan an gurfanar da shi tare da kamfaninsa Slok Nigeria Limited da kuma tsohon Daraktan Kudi na Gidan Gwamnatin Jihar Abia Jones Udeogu.
Daga bisani Udeogu ya daukaka kara zuwa Kotun Koli yana mai kalubalantar daurin da Babbar Kotun Tarayya ta yi musu.
A farkon watan jiya kuma Kotun Koli ta Najeriya ta soke daurin, tana mai cewa alkalin ba shi da hurumin yin haka saboda an yi masa karin girma zuwa Kotun Daukaka Kara a lokacin.
Ta kuma ce amfani da sashe na 396(7) na Dokar Hukunta Manyan Laifuffuka ta 2015 da aka dogara da shi aka bai wa Mai Shari’a Mohammed Idris damar zuwa ya kammala shari’ar ya saba wa Kundin Tsarin mulkin Najeriya.