✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba

An jaddada buƙatar amfani da sabon salo wajen yaƙar zamba, tare da bayyana yadda zamani ke buƙatar sababbin hanyoyin magance matsalolin laifukan kuɗi a duniya.

Jami’ar Sojojin Nijeriya da ke Biu (NAUB) ta ƙaddamar da taron magance zamba ta hanyar binciken fasaha karo na farko, wanda ya nuna ƙaruwar tasirin wannan jami’a a fagen ilimi a Nijeriya.

Taron ya gudana ne bisa taken “Kididdigar Forensic: Zuwa Ga Sabon Tsarin Magance da Gano Zamba,” wanda Farfesa Ahmad Imam, ƙwararre a fannin ƙididdigar kuɗi da magance zamba ya gabatar.

Tattaunawar ta jaddada dabarun zamani domin tunkarar zamba mai salo da kuma tsare-tsaren da za su taimaka wajen gano da magance laifukan kuɗi da ke ƙara ƙamari.

Shugaban Jami’ar NAUB, Farfesa Kyari Mohammed, ya bayyana wannan taro a matsayin wani muhimmin mataki ga jami’ar.

A cewarsa: “Abin alfahari ne mu yi bikin wannan muhimmin taro na farko, wanda ke nuna jajircewar NAUB wajen habaka ilimi da warware matsalolin al’umma.”

Shugaban Kwamitin Shirya Taron, Farfesa Adamu Isa Harir, ya bayyana taron a matsayin wata al’ada mai cike da tarihi a fagen ilimi.

Ya ce: “Wannan taro ba wai kawai nasara ce ga jami’a ba, har ila yau, yana nuna muhimmancin bincike da kirkire-kirkire wajen kawo sauyi ga al’umma.”

Farfesa Ahmad Imam ya jaddada bukatar sabon salo wajen yakar zamba, tare da bayyana yadda zamani ke buƙatar sababbin hanyoyin daidaitawa da matsalolin laifukan kudi a duniya da ke sauyawa cikin sauri.

A jawabin godiya, Magatakardar Jami’ar, Birgediya Janar H.Y. Abdulhamid, ya gode wa dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa wajen samun nasarar taron.

A cewarsa: “Muna matukar godiya da goyon bayan shugabannin jami’a da kuma kokarin ma’aikata wajen tabbatar da nasarar wannan taro.”

Haka kuma, Shugaban Sashen Kididdiga, Dakta S.J. Inyada, ya gabatar da kyauta ta musamman ga Farfesa Ahmad Imam a matsayin yabo kan gudunmawarsa a fannin kididdigar bincike ta hanyar fasahar zamani.

Dakta Inyada ya yaba wa Mataimakin Shugaban Jami’ar da shugabannin jami’a bisa jajircewarsu wajen inganta bincike da harkokin ilimi a jami’ar.

Wannan taro ba wai kawai ya zama wani babban ci gaba ga NAUB ba, har ila yau, ya tabbatar da alkawarin jami’ar na ci gaba da girmama bincike, kirkire-kirkire, da kawo sauyi mai ma’ana ga al’umma.

Wannan ya tabbatar da rawar NAUB a matsayin jagora wajen bunkasa bincike da ilimi a Nijeriya.