Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri.
Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar 4 ga watan Afrilun nan a yankin Ajari da Tashar Lara, inda matasan ɓangarorin biyu suka yi artabu da juna.
An daɓa wa wanda aka kashen wuƙa a ciki, wanda ba tare da ɓata lokaci ba jami’an tsaro na Maidugurin suka ɗauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa.
Wata majiyar ‘yan sanda ta ce, an kama wasu mutane bakwai masu shekaru tsakanin 15 zuwa 24.
Majiyar ta bayyana sunayen ababen zargin da aka kama da suka haɗa da Ba’abba Kyari mai kimanin shekara 20 sai Ali Alhaji Goni Ali dan shekara 20 da Muhammed Audu mai kimanin shekara 18, sai Ali Isa mai shekara 15 da Adam Sabir mai shekara 15 da Mohammed Tujja shekaru 17 da Usman Kasim dan shekara 24