An sako iyalan Alhaji Falalu Umar, Maharin Zazzau kuma Hakimin DutsEn Abba da ke karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna bayan da suka shafe kwana shida a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
A ranan Asabar din makon jiya ne da misalin karfe uku na dare masu satar mutane ne suna yin garkuwa da su suka yi wa gidan Hakimin da ke Dutsen Abba kawanya da manyan bindigogi suna harbe-harbe kafin su sace matarsa da ’ya’yansa maza biyu.
Aminiya ta ziyarci garin inda ta tarar da jama’a na ta tururuwa domin zuwa jajanta wa Hakimin da iyalansa, sai dai lokacin da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Hakimin game da yadda lamarin ya auku ya ce a gaskiya a yanzu ba zai iya cewa komai ba kan wannan lamari ba, sai dai a lokacin da iyalansa suke hannu wadanda suka yi garkuwa da su, yana magana da su, har zuwa lokacin da Allah Ya sa suka dawo gida yanzu haka suna gida bayan kwanaki da suka kwashe a hannun wadanda suka sace su.
Wakilinmu ya kuma yi kokarin jin ta bakin Masarautar Zazzau amma jami’anta ma sun ki cewa uffan aka lamarin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mukhtar Hussaini Aliyu da wakilinmu ya nemi jin ta bakinsa, ya ce a dan ba shi lokaci domin bai gama bincike a kan lamarin ba. Bayan nan ya sake kiransa har sau biyu amma bai dauki waya ba.
Wata majiya ta tabbatar wa Aminiya cewa sai da aka biya kudin fansa kafin a sako matar Hakimin da ’ya’yansa.