Mahaifiyar shugaban jam’iyyar Lebo, Misis Elizabeth Omotosho ta samu ’yancinta bayan da wadanda suka yi garkuwa da ita suka sako ta.
Aminiya ta gano cewa wadanda suka sace ta sun sake ta kuma tuni ta dawo gida a tsakar daren ranar Juma’ar da ta gabata.
Wasu ’yan bindiga su hudu sun sace Misis Omotosho, ’yar shekaru 71 a duniya, an sace ta a gidanta da ke garin Lobalade a yankin Tanke da ke garin Ilorin a daren Lahadin da ta gabata.