✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sako dan Majalisar Taraba da aka yi garkuwa da shi

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da Dan Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Hon. Bashir Muhammad, bayan kusan makon a hannunsu. Iyalan Hon. Bashir Muhammad sun…

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da Dan Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Hon. Bashir Muhammad, bayan kusan makon a hannunsu.

Iyalan Hon. Bashir Muhammad sun shaida wa Aminiya cewa a daren Asabar masu garkuwar suka sako shi ya kuma dawo gida.

Majiyarmu ta ce sai da aka biya kudin fansa da ba a bayyana yawansu ba kafin masu garkuwar su sako shi.

Da farko masu garkuwar sun kekashe kasa cewa sai an ba su Naira miliyan 150 kafin su sako shi, amma iyalansa suka ce allambaran, kafin daga baya bangarorin suka daidaita a ranar Juma’a.

Kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, DSP David Misal ya tabbatar wa Aminiya da labarin sako dan majalisar.

Tun bayan bullar labarin sakin Hon. Bashir Muhammad a safiyar Asabar, masoya da abokan arziki ke ta tururuwa zuwa gidansa domin yi masa barka da arziki.

%d bloggers like this: