✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako daliban Jami’ar Greenfield ta Kaduna

An sako daliban ne ranar Asabar bayan an biya wani adadi na kudin fansa.

Dalibai 14 na Jami’ar Greenfield ta Jihar Kaduna da ’yan bindiga suka sace daga dakunansu na kwana tun a watan Afrilun da ya gabata sun shaki iskar ’yanci.

An sako daliban ne ranar Asabar bayan an biya wani adadi na kudin fansa da ba a fayyace wa manema labarai ba.

Mai Magana da yawun jami’ar, Kator Yengeh ne ya inganta rahoton yayin zantawarsa da wakilnmu, sai dai ya ce Hukumar Gudanarwar jami’ar za ta fitar da karin bayani a nan gaba.

Da misalin karfe 8:15 na daren ranar 20 ga watan Afrilun da ya gabata ne aka sace daliban Jami’ar mai zaman kanta da ke kauyen Kasarami a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi garkuwa da dalibai 22 ne yayin da kuma wani ma’aikacin jami’ar ya rasa ransa.

Daga bisa ni ne ’yan bindigar suka bukaci naira miliyan 800 a matsayin kudin fansar dalibai, inda bayan kwana daya da sace su aka samu gawar biyar daga cikinsu yashe kusa da jami’ar.

Idan ba a manta ba, ’yan bindigar sun yi garkuwa da dalibai 22 a Jami’ar Greenfield, daga baya suka kashe biyar daga cikin daliban domin nuna wa gwamnati gazawarta kan cika sharudan da suka gindaya.

’Yan bindigar sun fara neman a biya su Naira miliyan 800 a matsayin kudin fansa, inda kwanaki uku bayan wa’adin nasu suka kashe uku daga cikin daliban, kafin daga baya suka kara kashe wasu biyu.

’Yan bindigar sun yi barazanar ci gaba da yi wa daliban kisan dauki dai-dai muddin ba a cika sharudan da suka bayar ba.

Aminiya ta ruwaito cewa, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ’yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban jami’ar sun fasa kashe su sabanin barazanar yin hakan da suka yi a baya.

Shehin malamin ya ce a yanzu sun shawo kan ’yan bindigar inda suka samu nasarar sauke su daga ra’ayin da suka rika na kashe daliban da ke hannunsu muddin aka gaza cika sharadin biyan kudin fansar da suka nema.