Daliban jami’ar harkokin noma ta Tarayya FUAM da aka sace a Jihar Benuwai sun shaki iskar ’yanci kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun jami’ar, Rosemary Waku ta fitar a ranar Laraba, ta ce dukkanin daliban sun kubuta ne a ranar Talata.
- Ya halasta mai azumi ya sha abun kara kuzari —Sheik Lawan Abubakar
- Za mu fara rushe gidajen masu taimakon ’yan daban daji — Matawalle
Kazalika, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Catherine Anene, ta inganta rahoto cikin wani gajeren sako da ta aike wa wakilinmu.
“An sako daliban jami’ar noma da aka sace cikin koshin lafiya kuma babu kudin fansa da aka biya kafin su kubuta,” a cewar Anene.
Sai dai dukkan bangarorin biyu basu bayar da wani bayani ba game da fansar naira miliyan 21 da aka yi zargin cewa ’yan bindigar sun nema gabanin sako daliban.
Aminiya ta ruwaito cewa, a Lahadin da ta gabata ce hukumar gudunarwar jami’ar da sanar cewa ’yan bindiga sun yi awon gaba da dalibanta da dama wanda ba a san adadinsu ba.