Dalibai 30 na makarantar FGC Birnin Yauri da ke Jihar Kebbi da malaminsu sun kubuta daga hannun kasurgumin dan bindigar nan Dogo Gide, bayan shafe kwana 207 a hannunsa.
An sako su ne bayan sun shafe wata shida cif.
- Karnuka sun ceto jaririyar da aka yasar tare da dumama mata jiki
- Magoya bayan APC sun kona tsintsiya a Gombe
A bara ne dai ’yan bindigar suka kai hari makarantar tare da sace daliban da wasu daga cikin malamai, lamarin da ya jefa iyaye da ’yan uwansu cikin alhini da fargaba.
Wadanda aka sako jiyan dai sune rukuni na karshe da suka kubuta daga hannun masu garkuwar.
Sai dai akwai rahotannin da ke cewa daya daga cikin daliban ya rasu lokacin da ake tsare da su.
Yahaya Sarki, wani hadimi ga Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ne ya sanar da kubutar da daliban a cikin wata sanarwa da maraicen Asabar.
Ya ce tuni aka kai daliban asibiti domin duba lafiyarsu, kafin a sada su da iyayensu.
Idan za a iya tunawa, a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba ne aka sako wasu 30 daga cikin daliban sannan aka kai su Birnin Kebbi kafin a hada su da iyayensu.
“Muna godiya ga dukkan jami’an tsaro da dukkan wadanda suka taimaka wajen kubutar da yaran, tare da jinjina ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari,” inji sanarwar.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana ko an biya kudin fansa ba kafin a kubutar da su ba.