✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An saki wata mata a Legas saboda ta saka wando

An saki wata matar aure a Jihar Legas, Fatimot Abiola ‘yar shekara 42 a rayuwa saboda ta saka wando. Mijin Fatimot mai suna Rasheed ya…

An saki wata matar aure a Jihar Legas, Fatimot Abiola ‘yar shekara 42 a rayuwa saboda ta saka wando.

Mijin Fatimot mai suna Rasheed ya sake matar ne duk da cewa sun kwashe kimanin shekara 22 da aure saboda ta ki bin umarninsa na kada ta sanya wandon.

Mai shara’a Mista Akin Akinniyi da yaba auren y ace ma’auratan sun gaji da zama tare domin ya yi duk mai yiwuwa domin shawo kan lamarin, amma abin ya ci tura.

Don haka ne ya bayar da umarnin a raba auren tun wuri, kafin lamarin ya kai ga cin mutunci.