✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An saki mutumin da ake zargi da kisan Jamal Khashoggi

Jami'an tsaro sun ce an samu bayan bogi ne yayin cafke mutumin.

Jami’an tsaro a birnin Paris na Kasar Faransa, sun saki mutumin da suka tsare kan zargin shi da hannu a kisan shahararen dan jaridar nan da kasar Saudiyya, Jamal Khashoggi.

Jami’an tsaron sun sallami mutumin ne bayan gudanar da bincike, inda suka ce an samu sabani ne har aka kama mutumin, saboda yana kama da wanda ake zargi da hannu a kisan Kashoggi.

An sanar da sakin mutumin ne bayan ya shafe sa’a 30 a tsare a filin tashin jirage na Charles De Gaulle da ke birnin Paris a ranar Laraba.

Jami’an tsaro sun ce sun dauka mutumin da ake nema ruwa a jallo ne mai suna Khalid Aedh al-Otaibi, bayan samun wasu bayanan sirri daga kasar Turkiyya.

Khalid Aedh al-Otaibi na daga cikin mutum 15 da ake zargi na da hannu a kisan Jamal Khashoggi a ranar 2 ga watan Oktoban 2018.