Iyalan Kansila mai wakiltar Mazabar Gwako ta Karamar Hukumar Gwagwalada a Abuja da wasu ’yan uwansa uku da aka yi garkuwa da su a kuayen Kpakuru sun shaka iskar ’yanci bayan an biya musu kudin fansa na naira miliyan hudu.
Aminiya ta ruwaito cewa, a Talatar makon jiya ne wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka afka gidan Kansilan mai suna Idris Muhammad, inda suka yi awon gaba da matansa biyu, kanwar daya da kuma wasu kannensa maza guda biyu.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da iyalan Kansila a Abuja
- Dalilin da na ziyarci Fulanin hanyar Kaduna zuwa Abuja —Dokta Gumi
- ’Yan ta’adda sun yi wa mafarauci yankan rago a Abuja
- An kashe ’yan bindiga 9 a hanyar Kaduna-Abuja
Daya daga cikin ’yan uwan Kansilan da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaidawa Aminiya cewa an saki iyalan Kansilan ne da misalin karfe 8 na dare bayan an kai wa masu garkuwar kudin fansa a Dajin Wumi da ke iyaka da Jihar Neja.
Ya ce, “Abun mamakin shi ne, bayan sun karbi kudin fansar a can kauyen Wumi, amma sai suka ce mu koma can Madakatar Giri, inda a nan ne muka samu ’yan uwan namu.”
“Sai dai muna yi wa Allah godiya kasancewar duk sun dawo gida cikin koshin lafiya,” inji shi.
Neman jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ya ci tura, a yayin da bata amsa kiran wayar da aka yi mata ba kuma bata bayar da amsar sakon kar ta kwana da aka aike mata da shi ba.