✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sake zabar Sergio Mattarella a matsayin shugaban Italiya

An shafe fiye da mako guda ana gudanar da zaben zagaye-zagaye.

An sake zabar Sergio Mattarella a matsayin Shugaban Italiya a wa’adi na biyu, bayan da shugabannin jam’iyya mai mulki a kasar suka yanke shawarar ya ci gaba da riko da akalar jagorancin kasar.

Zaben Mattarella da aka gudanar ranar Asabar a zauren Majalisar Dokokin kasar na zuwa ne bayan shafe mako guda ana kwan-gaba-kwan-baya wajen kada kuri’ar neman magajinsa.

Bayanai sun ce wannan lamari ya kawo kwanciyar hankali a siyasar kasar, bayan an shafe lokaci ana fargabar wajen neman wanda zai gaji kujerar Mattarella.

A ranar Asabar din ce dai gamayyar jam’iyyu masu kawance suka sanar da cimma matsaya daya na ganin sun sake zabar Sergio Mattarella.

Hakan dai na zuwa ne bayan ya amince zai karbi jagorancin kasar a wa’adi na biyu a cewar Ministar Harkokin Yanki da Iko a kasar, Mariastella Gelmini.

“Amincewar da Shugaba Sergio Mattarella ya yi na yin wa’adi na biyu, bisa bukatar mafi rinjayen jam’iyyun siyasa, ya nuna irin nauyin da ya rataya a wuyansa da kuma alakarsa da kasar da cibiyoyinta,” inji ta.

Sergio Mattarella

Mattarella mai shekaru 80 da haifuwa ya jima yana mai bayyana cewa zai sauka daga kujerar shugaban kasa, sai dai wannan yunkuri na sa na ganin jam’iyyun kasar sun zabi wani dan kasar a wannan matsayi bai tabbata ba.

Tun a zagaye na bakwai na zaben da aka gudanar Sergio Mattarella ya samu gagarumin goyan baya inda aka bayyana cewa ya samu kusan kuri’u 400, sai dai kundin tsarin mulkin kasar ta Italiya na bukatar dan takara a kujerar shugabancin kasar ya tattara kuri’u 505 domin samun nasarar zaben.

Sai dai a yayin zagaye na takwas inda fiye da ’yan majalisa da wakilan yankuna 1000 suka kada kuri’u, zauren Majalisar ya bude tafi da daga murya domin bayyana farin ciki bayan Mattarella ya samu kuri’u fiye da 505 da ake bukata na zama shugaban kasa.

A wani dan takaittace tsokaci da ya yi a zauren majalisar, Mattarella ya ce annobar Coronavirus da ake fuskanta da kuma matsin tattalin arziki da zamantakewa da kasar ke fama ya zama wajibi ya amince da shawarar da majalisar ta yanke.

Tuni dai Fafaroma Francis ya aike wa da Shugaba Mattarella sakon taya murna da fatan alheri.