Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta sanar da samun karin mutum biyar da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.
A cikin mutum biyar din dai an samu biyu ne a Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, biyu a jihar Legas, sai kuma daya a jihar Edo.
Biyu daga cikin sabbin wadanda suka kamu da cutar dai matafiya ne da suka dawo daga Birtaniya.
A wata tattaunawa da gidan talabijin na Channel, Darakta Janar na Hukumar ta NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu, ya ce matafiya da suka dawo daga kasashen da ke fama cutar ne kalubale a yanzu.
“Babbar barazanar da muke fuskanta daga matafiya ne masu dawowa daga kasashen da suke da wannan annoba, wadanda kuma aka bukaci su killace kansu na tsawon akalla kwanaki 14“.
Zuwa yanzu dai mutum 36 ne aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya, a cewar hukumar.