✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake saka dokar hana fita a jihar Osun

Ba zamu aminta da yadda da ake satar kayan gwamnati da na 'yan kasuwa da sauran mutanen jihar nan ba.

Kasa da sa’o’i 24 da dage dokar hana fita a jihar Osun, gwamnatin jihar ta sake saka dokar hana fita sakamakon yadda bata gari suke satar kayayyakin al’umma.

Bata gari sun ci gaba da fasa shaguna da satar kayayyakin mutanen jihar bayan janye dokar hana fita da gwamnatin jihar ta saka.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da yake jawabi ga mutanen jihar inda yace “gwamnati tayi allawadai da irin yadda ake satar kayan mutane, kwana daya bayan cire dokar hana fita”.

A cewarsa, “Ba zamu aminta da yadda da ake satar kayan gwamnati da na ‘yan kasuwa da sauran mutanen jihar nan ba”.

“Al’ummar jihar Osun ina mai sanar daku cewa mun sake saka dokar hana fita daga yanzu har zuwa lokacin da al’amura za su daidaita”.

Bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar, gwamnatin jihar ta yanke hukuncin sake saka dokar hana fita, domin samun damar shawo kan yadda abubuwa suka tabarbare.