✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sake kone ofishin INEC a Imo

Karo na biyu ke nan da ake kai wa ofishin hari cikin kwana uku

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce an sake kai hari tare da kone ofishinta da ke Karamar Hukumar Orlu ta Yamma a jihar Imo.

Kwamishininan hukumar mai kula da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma aka wallafa a shafin hukumar na Twitter ranar Lahadi.

A cewarsa, “Kwamishinan hukumar a jihar ta Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu ne ya ba hukumar rahoton kai harin wajen misalin karfe 4:00 na Asubahin Lahadi, hudu ga watan Disambar 2022.

“An kai harin ne kan dakin taro na hukumar, inda aka kone kujeru da tebura da sauran abubuwa. Sai dai muhimman kayayyakin da ke ciki lamarin bai shafe su ba,” inji Festus Okoye.

Ya ce ko a ranar Alhamis din da ta gabata sai da aka kai hari ofishin hukumar.

“Wannan shi ne karo na bakwai da ake kai wa ofisoshinmu a jihohi biyar da ke fadin kasar nan a cikin wata hudu da suka gabata,” inji Festus Okoye.

Ana dai ci gaba da fargabar kai hare-hare kan ofisoshi da kayyakin INEC a jihohin Kudu maso Gabas, inda ake zargin ’yan awaren Biyafara ta IPOB da kai su.

Da yake tsokaci a kan lamarin, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira da a gaggauta yin bincike don hukunta masu hannu a ciki.

Ko a cikin makon da ya gabata sai da Farfesa Yakubu ya ce hare-haren da ake kai wa kayayyakinsu sam ba za su shafi ingancin zaben da za su gudanar a Najeriya a 2023 ba.