✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sake kashe biyu daga cikin daliban jami’ar da aka sace a Kaduna

Kasa da mako guda bayan ’yan bindigar sun jefar da gawar uku daga cikin daliban Jami'ar

’Yan bindigar da suka sace daliban Jami’ar Greenfield da ke Jihar Kaduna sun sake kashe biyu daga cikin daliban.

Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida, Samuel Aruwan ya fitar ta ce an tsinci gawar daliban ne a ranar Litinin.

“Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai tana bakin cikin wannan aika-aikan da aka yi wa daliban da ba su ji ba, ba su gani ba, bayan an sace su yayin da suke neman ilimin domin samun makoma mai kyau.

“Gwamnatin tana mika ta’aziya ga mahukunta Jami’ar da kuma iyayen daliban da lamarin ya shafa, tana mai rokon Mai Duka ya jikan su,” inji Aruwan.

A makon da muka yi bakwana da shi ne ’yan bindigar suka kashe uku daga cikin daliban da suka ce a ranar Talatar da ta gabata.

Aminiya ta ruwaito cewa, wasu gungun ’yan bindiga ne suka kai hari jami’ar da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka sace dalibai da dama da kuma ma’aikata.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 10.30 na dare a Talata, inda maharan rike da makamai suka harbe wani mai gadi a Jami’ar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da sace daliban, sai dai a wancan lokaci ya ce ba a san adadin daliban da ’yan bindigar suka diba ba.